Kotun daukaka kara ta soke sallamar dan majalisan PDP a Osun

Kotun daukaka kara ta soke sallamar dan majalisan PDP a Osun

Rahotanni sun kawo cewa an tabbatar da nasarar Bamidele Salam, dan majalisa mai wakiltan Ede ta Arewa, Ede ta Kudu, Egbedore, Ejigbo na Osun a majalisar wakilai.

Kotun daukaka kara da ke zama a Akure, jihar Ondo ce ta tabbatar da nasarar zaben Salam, a ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Justis Muhammed Danjuma, wanda ya sauya hukuncin kotun zabe da ta yanke a anar 2 ga watan Satumba, ne ya kaddamar da ukuncin kotun.

Kotun daukaka karar a hukunta ta bayyana cewa kotun zaben tayi kuskuren amfani da dokar zabe wajen yanke shawara kan zarcewar kuri’u.

Justis Danjuma, yayinda yake karanto hukuncin, ya kuma bayyana cewa jawaban da aka gabatar a gaban kotun zaben bai tabbata da zargin mai karan ba.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Dillalan motoci sun zargi hukumar kwastam na Najeriya da rashawa

Da yake martani akan hukuncin kotun, Salam yace tsarin doka akan lamarin zaben na tattare da kalubale.

Da yake sadaukar da nasararsa ga Allah da yan Najeriya baki daya, Salam yace Allah ne kadai ya san dalilin da yasa irin wannan kotun zabe ya fada a kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel