Kuma dai! Ghana ta sake rokan Najeriya ta taimaka ta bude iyakokinta

Kuma dai! Ghana ta sake rokan Najeriya ta taimaka ta bude iyakokinta

Mataimakin ministan harkokin wajen Ghana, Mista Charles Owiredu, a jiya ya gana da karamin ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Zubairu Dada, kan cigaba da rufe iyakokin Najeriya da kasashen makwabta.

Wannan ganawar ya biyo bayan ganawar da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, da takwararsa na Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey , ministan kasuwancin Ghana, Alan Kyerematen.

A ganawar Ambasada Dada da Owiredu, sun tattauna kan hanyoyin kawar da kalubalen da yan kasuwan Ghana dake kokarin shigo da kayayyakinsu Najeriya ke fuskanta sakamakon kulle iyakokin kasa.

Ambasada Dada ya tabbatarwa takwararsa na Ghana cewa wannan Najeriya ba tayi nufin cutar da Ghana ba, kawai tana kokarin magance matsalolin da take fuskanta ne cikin gida.

Dada ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawaran rufe bodan ne na dan kankanin lokaci saboda yadda ake fasa kwabrin kayayykin haram cikin kasar.

Mun kawo muku rahoton cewa 'yan kungiyar 'yan kasuwar kasar Ghana a ranar Alhamis sun rufe shagunan 'yan Najeriya a kasuwanni 5 dake ke Kumasi, yankin Ashanti na babbar birnin kasar.

Wannan ne karo na biyu a cikin shekarar nan da kungiyar ke rufewa 'yan Najeriya shagunansu da ikirarin neman fada da bakin hauren da ke yin irin kasuwancinsu a kasar tasu.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa, bakin hauren sunyi karantsaye ne ga sashi na 27 na dokokin cibiyar habaka hannayen jari ta kasar Ghana. Dokar kuwa ta haramtawa bakin haure siyar da kayansu ko tallata hajojinsu a duk wata kasuwa ko tarin shagunan da aka ware don 'yan kasar Ghana din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel