Wata sabuwa: Dillalan motoci sun zargi hukumar kwastam na Najeriya da rashawa

Wata sabuwa: Dillalan motoci sun zargi hukumar kwastam na Najeriya da rashawa

Dillalan motoci wadanda hukumar kwastam na Najeriya suka rufe ma shaguna a Lagas sun zargi hukumar da rashawa da kuma rufe masu harabar kasuwancinsu ba bisa ka’ida ba.

A ranar 30 ga watan Satumba, jami’an hukumar kwastam na Najeriya sun kai mamaya sannan suka rufe shagunan dillalan motoci a Lagas ba tare da basu takardar sanarwa ba.

A wani taron manema labarai a Lagas a ranar Alhamis, yan kasuwan sun nuna damuwa akan kulle shagunansu da aka yi tsawon wata guda da ya gabata.

Farmakin da hukumar kwastam ta kai wa dilallan mota a fadin kasar ya kasance domin gane motocin da aka yi fasa kaurinsu da kuma motocin da ba a biya haraji ba.

Dillalan motocin sun gudanar zanga-zanga a taron manema labaran.

“Muna cikin wani hali, sama da wata guda da ya gabata, babu kasuwanci,” daya daga cikin yan kasuwan ya koka a taron.

Morgan Ogbede, Shugaban kungiyar dillalan motoci a Lagas, yace yan kasuwan sun gaji da yadda suke fuskantar matsi, barazana da tozarci daga hannun jami’an kwastam tsawon shekaru da dama.

Yace jami’an kwastam na tatse kwastamominsu a hanyoyi yayinda suke tafiya da motocin da suka siya a wajen Lagas. Yace hakan yayi sanadiyar da suka daina samun ciniki daga mutane a wajen Lagas.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta koka akan zaryan yan bindiga daga Zamfara, Katsina zuwa sauran jihohi

Adebayo Adenihun, wani dillalin motoci yace wasu daga cikin jami’an kwastam na yiwa gwamnati yankan bakin aljihu domin dillalan motoci basa kin biyan haraji.

Ya nemi a binciki jami’an da ke duba motoci a tashoshin jirage. Ya yi zargin cewa idan suka biya naira miliyyan daya, 600,000 ake rubutawa a jikin risit.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel