Da walakin goro a miya: Sanatoci sun fara neman kulla kyakkyawar alaka da Sadiya

Da walakin goro a miya: Sanatoci sun fara neman kulla kyakkyawar alaka da Sadiya

Tsarin bayar da tallafi ga matasa marasa aikin yi, watau N-Power, da tsarin tallafa ma yan Najeriya gajiyayyu da masu rauni da N5000 a duk wata, TraderMoni da kuma tsarin ciyar da daliban firamari na fuskantar wata sabuwar kalubale daga yan majalisa.

Idan za’a tuna gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta kirkiro wadannan ayyuka da wasu ma da dama da zummar taimaka ma yan kasa, inda Maryam Uwais ke kula dashi a karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

KU KARANTA: Majalisa ta tantance shuwagabannin hukumar NDDC da Buhari ya tura mata

Sai dai a yanzu jarida The Cables ta ruwaito Buhari ya dauke aikin daga ofishin Osinbajo ya mika ma sabuwar ma’aikatar kula da bala’o’i da cigaban jama’a dake karkashin Hajiya Sadiya Umar Faruk, wanda yan majalisa suka hura ma wuta domin neman yagar rabonsu.

Wannan bukata ta yan majalisa ta fito fili ne a ranar Juma’a, 25 ga watan Oktoba yayin da ministar tare da Uwais suka bayyana gaban yan majalisun domin su kare kasafin kudinsu daya kai naira biliyan 500, amma kafin a fara zaman sai yan majalisun suka nemi yan jarida dake yanar gizo su fice su basu wuri.

Bayan kammala zaman, wani dan majalisa ya tsegumta ma majiyarmu cewa: “Takwarorina sun zargi Uwais da mayar damu saniyar ware, bata yi damu musamman wajen bada kwangila, da kuma bamu guraben aiki, don haka suka yi alkawarin zasu yi maganinta, shi yasa basu barta ta yi magana ba.”

Sanatan ya tabbatar da cewa minista Sadiya kadai aka bari ta yi magana, wanda kuma ta yi magana cikin sansanyan murya, tare da girmamawa, wanda yasa Sanatocin suka ji dadi, hakan tasa zaman kare kasafin kudin ya gudana cikin sauki da dadi a ranar Litinin.

Babbar damuwar dake damun yan Najeriya a yanzu shine kada tsarin bayar da tallafin ya zamto kamar tsare tsaren gwamnatocin baya da basu cimma manufofinsu ba saboda rashawa da kuma rashin kyakkyawar tsari, domin kuwa masana sun ittifakin cewa babu wani tsarin tallafi daya taba yin tasirin da N-Power da sauran suka yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel