Ebonyi: David Umahi ya sallami Ndubisi Itumo daga aiki - SSG

Ebonyi: David Umahi ya sallami Ndubisi Itumo daga aiki - SSG

- Gwamna Dave Umahi ya tsige wani Hadiminsa daga aiki

- Itumo ya yi abin da ya jawo masa fushin Mai gidan na sa

- Sakataren gwamnati ya shaida sauke Itumo daga mukami

Mai girma gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya kori Hadiminsa daga bakin aiki bayan ya fitar da wani jawabi ba yadda ya dace ba. A tsakiyar makon nan ne aka bada wannan sanarwa.

Sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, Dr. Kenneth Ugbala, shi ne ya fitar da jawabi ya na mai sanar da tsige Mai taimakawa gwamnan daga aiki a Ranar Larabar nan, 30 ga Watan Oktoba, 2019.

Kenneth Ugbala ya shaida cewa Ndubisi Itumo zai bar aikin ne ba tare da wani wata-wata ba. A baya Ndubisi Itumo ya kasance Mai taimakawa gwamna a kan kafafen sadarwa na zamani.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta kai Yara karatu manyan Jami’o’in waje

“Sallamar ta zo ne a dalilin rashin bin doka na yada bayanan da su ka batar da jama’a. Bayan haka, an umarci Itumo ya mika duk wasu kayan gwamnati da ke hannunsa zuwa ga PPS.”

Jawabin da ya fito daga ofishin SSG ya bukaci tsohon Mukarrabin na gwamna Umahi ya maida duk wasu dukiyoyi da kayan aikin da ke ofisinsa a hannun babban Sakataren gwamnan jihar.

Mista N. Itumo ya shiga cikin sahun Hadiman da su ka rasa kujerunsu a gwamnatin Dave Umahi a wannan wa’adi. Kwanakin baya dai gwamnan ya yi zazzagar da ta shafi kusohin jihar Ebonyi.

Jawabin sallamar bai bayyana ainihin laifin da Ndubisi Itumo ya aikata ba. Kwanakin baya dai gwamnan ya gargadi Masu taimaka masa da su guji sukar shugaba Buhari ko su rasa aikinsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel