Gwamnatin tarayya ta koka akan zaryan yan bindiga daga Zamfara, Katsina zuwa sauran jihohi

Gwamnatin tarayya ta koka akan zaryan yan bindiga daga Zamfara, Katsina zuwa sauran jihohi

Gwamnatin tarayya ta koka kan sauya wuri da yan bindiga da suka ki ajiye makamansu ke yi daga jihohin Zamfara da Katsina zuwa jihohin dake makwabtaka da gaba da su.

Sakatariyar dindindin, na ayyuka na musamman a ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya, Dr Amina Shamaki, wacce ta bayyana hakan a taron tsaro na tarayya da jihohi a Jalingo, ta ce hakan nuni ne ga cewar yan bindigan da basu sadufa ba suna kokarin yada annobar zuwa sauran yankuna.

Ta bayyana cewa wasu jihohi a arewa ta tsakiya da kudu maso yamma sun fara fuskantar matsala ta fannin garkuwa da mutane wanda wadannan yan bindiga suka fara yadawa a yankunan.

Shamaki ta karfafa wa hukumomin tsaro gwiwa akan su jajirce a kokainsu na kasa-kasa da yan bindiga sannan su hana su yancin yin yawo da aiwatar da ayyukansu.

Sakatariyar ta yaba ma gwamnonin jihohin Taraba da Benue akan kokarinsu na kawo mafita mai dorewa kan ikicin Tiv/Jukun a jihar Taraba.

A cewarta, gwamnoni na aiki tare da gwamnatin tarayya domin kawo mafita ta hanyar gina tsarin zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, sun ceto mutum 8 a Kaduna

Shamaki ta kuma bukaci sauran gwamnoni dasu marawa gwamnatin tarayya baya wajen magance annobar rikicin addini da na kabilanci a sauran yankunan kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel