Jami’an yan sandan Kaduna sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane sannan sun ceto mutane takwas, ciki harda matashi dan shekara 13 a tsakanin ranakun Talata da Alhamis a wasu ayyuka daban-daban da suka gudanar a jihar.
Lamain ya afku ne a Rigasa dake karamar hukumar Igabi na jihar sannan dayan kuma a Narayi, karamar hukumar Chikun na jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Yakubu Sabo, wanda ya bayyaa hakan a wani jawabi a ranar Juma’a, yace kamun kasurgumin dan ta’adda ya yi sanadiyar ceto mutane takwas da ke a hannun masu garkuwa da mutane a wurare daban-daban a jihar.
A cewar kakakin yan sandan, mai laifin, wanda aka bayar da sunansa a matsayin Mustapha Ibrahim, na taimaka wa yan sanda a bincikensu yayinda sauran mambobin kungiyar suka ci na kare.
KU KAANTA KUMA: Kuma dai: An gano wasu yara 2 da aka sace a Gombe a Anambra
Sabo ya kuma bayyana cewa ami’an rundunar sun zazzage sansanonin yan bindiga a dajin Maguzawa da Gurguzu da ke jihar sannan sun yi musayar wuta da yan bincigan, wanda aka ce da dama daga cikinsu sun tsere da raunukan bindiga.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng