Jam'iyyar APC ta dakatar da zababen dan majalisar ta da ya ki zuwa a rantsar da shi

Jam'iyyar APC ta dakatar da zababen dan majalisar ta da ya ki zuwa a rantsar da shi

A jiya ne jam'iyyar APC a karamar hukumar Okada ta gabas a jihar Edo ta dakatar da dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Ovia ta Arewa maso gabas.

Shuwagabannin jam'iyyar sun zargi dan majalisar ne da haramta musu wakilcin da ya da ce a majalisar jihar.

Vincent Uwadiae na daga cikin 'yan majalisa 14 da aka zaba amma suka ki kai kansu don rantsarwa a majalisar jihar.

Legit.ng ta gano cewa, tuni Uwadiae ya tattara komatsansa ya koma babban birnin tarayya tun bayan da aka zabeshi.

DUBA WANNAN: Shari'ar Buhari da Atiku: Tambuwal ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun koli ta yanke

Dakatar da shi din na kunshe ne a wasikar da shugaban jam'iyyar, Anselm Ojezua yasa hannu tare da Chief Etinosa Ighodaro da sauran shuwagabannin jam'iyyar.

An gano cewa, an zargi Uwadiae ne da laifin haramtawa kansa zaman majalisar.

"Bamu amince da rashin ganin Vincent Uwadiae ba a majalisar jihar Edo. Rashin zuwansa taron ranar 15 ga watan Oktoba da aka yi don bashi umarnin komawa majalisa ya ci karo da dabi'un mutanen Ovia. Muna kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da ta duba tare da kiran Uwadiae," In ji wasijar.

Idan za a tuna, a satin da ya gabata an gurfanar da dan majalisar akan laifuka 6 da suka hada da rashin halartar zaman majalisar, da wasu laifuka.

Jastis Oviagele ya dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba tare da umartar Sifeta Janar din 'yan sanda da ya kawo dan majalisar kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel