Majalisa ta tantance shuwagabannin hukumar NDDC da Buhari ya tura mata

Majalisa ta tantance shuwagabannin hukumar NDDC da Buhari ya tura mata

Majalisar dattawa ta tantance wasu mutane uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika mata da sunayensu domin ta tantancesu kafin ya nadasu mukamin shuwagabannin hukumar kula da cigaban yankin Neja Delta, NDDC.

Jaridar Guardian ta ruwaito mutanen uku sun hada da Pius Odubu, Cif Bernard Okumagba da Otobong Ndem. Shugaba Buhari ya nemi majalisar ta amince da nadin Pius a matsayin shugaban hukumar gudanarwar NDDC.

KU KARANTA: Neman kudaden shiga: Gwmanatin Kaduna za ta fara safarar masara da citta zuwa kasashen Turai

Yayin da ya nemi majalisar ta tantance Bernard domin kasancewa darakta a hukumar da kuma Otobong a matsayin babban darakta mai cikakken iko mai kula da sashin gudanar da manyan ayyuka.

A lokacin daya bayyana gaban majalisar, Mista Pius Odubu, tsohon mataimakin gwamnan jahar Edo ya bayyana mata manufarsa na amfani da wannan dama domin kawo karshen tashe tashen hankula da matasa ke janyowa a yankin Neja Delta.

Amma da aka zo kan Bernard Okumagba, sai yan majalisun suka nemi ya ‘rusuna ya tafi’ saboda cancantarsa da kuma kwarewarsa da suka sanyashi dacewa da wannan mukami. Sai dai da aka zo kan Otobong an dan samu hatsayin yayin tantance shi.

Wani dan majalisa mai suna Sanata Mathew Urhoghide ne ya bayyana cewa bai gamsu da yadda Otobong ya jera bayanan karatunsa a cikin takardar bayanansa na neman aiki ba, amma dai daga bisani an kwantar da hatsaniyar, kuma majalisar ta amince da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel