Buhari ya dakatar da albashin kafatanin malaman jami’o’in Najeriya

Buhari ya dakatar da albashin kafatanin malaman jami’o’in Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta cika alkawarin data dauka na dakatar da albashin duk wani ma’aikacin gwamnatin tarayya da bai yi rajista da tsarin albashi na IPPIS ba, inda ta fara da malaman jami’a.

Jaridar Guardian ta ruwaito gwamnatin Najeriya ta hana malaman jami’o’in Najeriya albashinsu na watan Oktoba sakamakon tirjiya da kungiyarsu ta ASUU ta nuna game da umarnin gwamnati na shiga karkashin tsarin IPPIS.

KU KARANTA: Neman kudaden shiga: Gwmanatin Kaduna za ta fara safarar masara da citta zuwa kasashen Turai

Idan za’a tuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ma yan majalisun dokokin Najeriya yayin daya mika musu kasafin kudin shekarar 2020 cewa ya bada umarnin dakatar da albashin duk wani ma’aikacin gwamnati da bai shiga tsarin IPPIS ba.

An ruwaito ministar kudi, Zainab Ahmad tana fadin cewa: “Bai kamata ASUU ta shiga yajin aiki saboda wannan batu ba, a fahimtarmu abinda ASUU take nufi shine a fifita ta fiye da sauran ma’aikatan gwamnatin tarayya da suke cikin tsarin IPPIS, zamu cigaba da tattaunawa dasu, amma dai ni kam shugaban kasa ya riga ya bani umarni.”

Haka zalika wani babban jami’I a ma’aikatar kudi ya bayyana cewa babu abinda gwamnati za ta fasa in dai a kan maganan IPPIS ne, saboda a yanzu haka tsarin ya yi nisa, kuma ASUU bata isa ta hana ba, don haka aka dakatar da albashinsu kamar yadda shugaban kasa ya umarcemu.

Jami’in yace abinda yasa ASUU take wannan tirjiya shi ne saboda malaman jami’a sun saba karbar albashi daga jami’o’I da dama. Baya ga jami’ar da aka daukesu aiki, suna fita wasu jami’o’I na daban suna aikin wucin gadi, kuma tsarin IPPIS bai yarda da wannan ba.

A wani labarin, kungiyar ASUU ta sanar da janye shirinta na shiga yajin aiki da ta yi niyyar faraway idan har gwamnatin Najeriya ta dakatar da albashinta saboda ta ki amincewa da tsarin IPPIS. Shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ne ya sanar da haka inda yace sun fara tattaunawa da gwamnati a kan wani sabon tsari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel