Yadda muka kama barawon dake amfani da asusun banki 51 – Ibrahim Magu

Yadda muka kama barawon dake amfani da asusun banki 51 – Ibrahim Magu

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa zuwa yanzu sun kaddamar da cikakken bincike a kan kasurgumin barawon nan Ismaila Mustapha wanda ya shahara wajen damfara da satar kudi ta yanar gizo.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Magu ya bayyana cewa Ismail Mustapha wanda ake kira da suna Momph ya saci makudan kudade da suka kai naira biliyan 14 ta kamfaninsa mai suna Imalob Global Investment Limited, sa’annan yana amfani da asusun ajiyan kudi na banki guda 51.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano a fadar gwamnati

Magu ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a ofishin EFCC dake jahar Kano, inda yace Mompha ya mallaki kadarori da dama a Dubai, baya ga agoguna guda 5 da aka kwace daga hannunsa da suka kai naira miliyan 60.

“Kama Ismaila Mustapha Mompha da abokin ta’asansa Hamza Koudeih saboda hannu da suke dashi cikin zamba, damfara da satar kudi ta yanar gizo, babban nasara ne a garemu, kama mutanen ya bamu kwarin gwiwa a yakin da muke yi da rashawa.

“Haka zalika shi ma abokin ta’asansa, Koudeih yana da wasu kamfanoni guda biyu, THK Services da CHK Properties wanda ya yi amfani dasu wajen satar kudi naira biliyan 19. Koudeih na zama ne a wani dakin alfarma a Otal din Eko Atlantic Pearl Tower Victoria Island inda yake biyan dala miliyan 5 a shekara.” Inji shi,.

Daga karshe Magu yace sun fara binciken wayoyin mutanen biyu domin hako bayanai da zasu taimaka musu wajen bincikensu, kuma da zarar sun kammala binciken zasu gurfanar dasu gaban kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel