Boko Haram ta razana al'ummar jihar Ondo

Boko Haram ta razana al'ummar jihar Ondo

Tsoro ya shiga zukatan mutanen birnin Akure da Owon na jihar Ondo a jiya sakamakon jita-jita da aka dinga yadawa cewar 'yan ta'addan Boko Haram suna shirin kai farmaki a wasu bankunan jihar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Shirin kai farmakin na kunshe a wata takardar da aka rubuta ga kwamishinan 'yan sandan jihar, Undie Adie, a cewar wata hukumar tsaro.

A halin yanzu takardar ta bazu a kafafen sada zumunta.

Adie ya yi kira ga jami'an 'yan sanda da su yi duk abinda ya dace a kan barazanar.

Takardar mai kwanan wata 29 ga watan Oktoba tana da taken, 'Shirin fashi ga wasu bankuna a jihar Ondo daga wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne.'

Kamar yadda takardar ta bayyana: "Bayanan sirri da hukumar ta samu ya bayyana cewa akwai shirin fashi da makami ga wasu bankuna a jihar Ondo daga 'yan ta'addan da ake zargin Boko Haram ne,"

DUBA WANNAN: Mutuwar Al-Baghdadi: Kungiyar ISIS ta yi sabon shugaba

"Kungiyar na shirin garkuwa da mutane da kuma kwace motoci a manyan titunan jihar. Yankunan sun hada da Owo zuwa Benin, Isua zuwa Ikare da Auge zuwa Ayire don samun kudin da zasu dau nauyin ta'addancinsu a fadin kasar nan.

"An gano cewa, 'yan ta'addan dake tsakanin Kogi zuwa Ondo sun kammala shirin yin babban fashi da makami a karamar hukumar Owo, jihar Ondo a ranar 1 ga Satan Nuwamba, 2019, wacce take ranar kasuwa."

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Femi Joseph, yace 'yan sandan basu samu wata takarda mai kamar haka daga wata cibiyar tsaro ba.

Ya ce: "Hukumar bata san da wata takarda mai taken shirin kawo farmaki daga Boko Haram ba a jihar. A don haka ne hukumar ke kokarin ganin ta tabbatar da isasshen tsaro ga rayuka da kadarorin mutanen jihar."

Ya kara da cewa, "Hukumar shirye take wajen bayar da tsaro isasshe a cikin watannin nan na karshen shekara ga duk sako da lungunan jihar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel