Wasu barayi sun yi wa masu gida 'wulankanci' a ban-daki bayan sun kasa shiga cikin gidan su yi sata

Wasu barayi sun yi wa masu gida 'wulankanci' a ban-daki bayan sun kasa shiga cikin gidan su yi sata

Wasu barayi da su ka yi yunkurin shiga wani gida a Uyo, Akwa Ibom sunyi wani abin takaici - sunyi bayan gida cikin wurin da ake wanka a ban-daki kafin su fice daga gidan.

Mai gidan, wani dan kasuwa da ya ce sunansa Nkereuwen da ke zaune da matarsa da 'ya'yansa a gidan a Obio Imo Street a Uyo ya shaidawa Premium Times a ranar Alhamis cewa akwai yiwuwar barayin sun aikata hakan don su 'hukunta' shi duba da cewa ba su samu ikon shiga uwar-dakarsa ba.

Lamarin ya faru ne makonni biyu da suka gabata misalin karfe 10 na safe yayin da mutanen unguwan sun tafi wurin sana'o'insu saboda haka babu hayaniya a unguwar.

DUBA WANNAN: Shari'ar Buhari da Atiku: Tambuwal ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun koli ta yanke

Mista Nkereuwem ya ce, "Duk da cewa ban dakin yana kusa da uwardaka, kofofin shiga daban ne. Da ya ke ba mu rufe kofar ban-dakin da kyau ba sun samu ikon shiga. Amma ina tunanin sun fusata ne bayan sun kasa shiga uwar daka da sauran dakunnan gidan. Hakan ya sa suka tafka wannan aika-aikan."

Ya kara da cewa, "Akwai ban-daki a nan, da nan za suyi amfani da shi idan dai ba sun so su hukunta ni bane.

"Sun kuma watsa katsa a cikin ban-dakin. Dole sai da mai daki na ta wanke wurin baki daya da muka dawo gida da yamma a ranan da abin ya faru."

Mista Nkereuwem ya kuma ce barayin da suka shigo gidansa makonni kadan da suka wuce sun sace masa rediyo da batirin motarsa.

A 'yan kwanakin nan rundunar 'yan sanda a jihar ta ce ta samu labarin sace-sace da ake yi a garin.

Sanarwar da mai magana da yawun 'yan sanda, Odiko MacDon ya fitar ya ce, "Abin da ya fi damunsu shine babu wanda ya kira su ya shigar da rahoto (kan afkuwar wadannan abubuwan), hakan ya sa batagarin ke cin karensu ba babbaka."

Ya ce lambar wayarsu a bude ta ke a koyaushe amma dai ba zai yi wu 'su kasance a ko ina a lokaci guda ba.'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel