Jami'an tsaro sun tseratar da wasu mutane 15 cikin mari daga wata majami'a

Jami'an tsaro sun tseratar da wasu mutane 15 cikin mari daga wata majami'a

Mutane 15 ne masu shekaru daga 19 zuwa 50 aka tseratar a daren ranar Alhamis daga wani sashin 'horo' da ke wata majami'a a Isheri - Osun, Egbe Idimu LCDA da ke Legas.

Majami'ar da ke lamba 26, titin Alafia, Oriofe Ijegun Isheri, sanannen guri ne da suka kware da raba tubaraki tare da warkarwa karkashin jagorancin wani 'manzo' mai suna Joseph Ojo mai shekaru 58 a duniya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An gano cewa, mutanen da aka saka a marin da suka kunshi maza da mata, suna cikin sarkokin ne sama da shekaru hudu. A halin yanzu wadanda aka tseratar din da kyar suke iya tafiya.

An gano cewa, wasu daga cikin mutanen na fama da matsanancin rashin lafiya kuma iyayensu ne suka mika su ga majami'ar don samun waraka.

'Yan sandan da suka kai samame da misalin karfe 6:10 na yammacin ranar Alhamis, sun cafke Ojo tare da wasu mutane 10 da suke zargin da sa hannun a aika-aikar.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APC ta zargi jami'an 'yan sanda da tarwatsa musu taro a Zamfara

Kamar yadda mai magana da yawun 'yan sanda ya sanar, DSP Bala Elkana yace, an gano cewa 'manzon' ya kasance a wannan majami'a tun a shekarar 1986. An kuma sakasu a marin ne don gudun tserewarsu.

Ya ce: "Wasu daga cikin mutanen sunyi shekaru biyar a daure. Akwai masu shekaru daga 19 zuwa 50 a duniya. Wasu daga cikinsu danginsu ne suka kawosu don samun waraka daga hauka da sauran cutuka. Manzon ya ce, yana wannan aikin ne tun 1986,"

"Ana cigaba da bincike. Jami'an tsaro na aiki tare da cibiyoyin gwamnati don samar da lafiya ingantacciya da kuma wajen kwana ga wadanda abin ya shafa," in ji Elkana.

Jaridar The Nation ta ruwaito hakan ne a lokacin da jami'an 'yan sanda ke ta kai samame ga gidajen horarwar addini a jihar Kaduna da wasu jihohin arewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel