Bidiyo: An kama almajirai da suke yaudarar mutane ta hanyar sanya ciwon karya a jikinsu don a basu sadaka

Bidiyo: An kama almajirai da suke yaudarar mutane ta hanyar sanya ciwon karya a jikinsu don a basu sadaka

- An kama wasu almajirai da suke sanya ciwon karya a jikinsu su yaudari mutane

- An kama almajiran ne dai a jihar Legas, inda aka tilasta daya daga cikinsu ya ciro kayan da yake hada wannan abu da shi

- Tsananin talauci da yunwa ta sanya mutane na kara fita yawon bara da almajiranci

An kama wasu mabarata a jihar Legas da suke hada ciwon karya suna yaudarar mutane da shi ana ba su sadaka.

A wani bidiyo da @gidifeedtv ta wallafa a shafin Twitter yau Alhamis dinnan, namijin da aka kama an tilasta shi ya cire duka kayan da yake amfani da su wajen hada wannan ciwo na shi.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san ainahin inda wannan lamarin ya faru ba a jihar ta Legas, kuma ba a san kowanene mabaracin ba.

KU KARANTA: Kano ta Dabo tumbin giwa: An yi shagalin bikin sunan wata akuya da ta haihu a jihar Kano

Tsananin talauci da yunwa ta sanya mutane na kara fita yawon bara da almajiranci, inda a yanzu haka ake hasashen cewa almajiran da suke bara a yanzu sun linka wadanda suke a baya.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel