Wata sabuwa: Kungiyar 'yan kasuwan Ghana ta rufe shagunan kasuwancin 'yan Najeriya

Wata sabuwa: Kungiyar 'yan kasuwan Ghana ta rufe shagunan kasuwancin 'yan Najeriya

'Yan kungiyar 'yan kasuwar kasar Ghana a ranar Alhamis sun rufe shagunan 'yan Najeriya a kasuwanni 5 dake ke Kumasi, yankin Ashanti na babbar birnin kasar.

Wannan ne karo na biyu a cikin shekarar nan da kungiyar ke rufewa 'yan Najeriya shagunansu da ikirarin neman fada da bakin hauren da ke yin irin kasuwancinsu a kasar tasu.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa, bakin hauren sunyi karantsaye ne ga sashi na 27 na dokokin cibiyar habaka hannayen jari ta kasar Ghana. Dokar kuwa ta haramtawa bakin haure siyar da kayansu ko tallata hajojinsu a duk wata kasuwa ko tarin shagunan da aka ware don 'yan kasar Ghana din.

Hakazalika, dokar ta haramtawa bakin haure yin sana'ar hayar tasi, bude wajen gyaran jiki, siyarda magunguna, hadawa ko siyarda ruwan leda da sauransu.

DUBA WANNAN: Waiwaye: Martanin Buhari bayan kotun koli ta yi watsi da karar da ya daukaka a an zaben 2011

Kasuwannin da aka rufewa 'yan Najeriya shagunan sun hada da kasuwannin Kejetia, Suame Magazine, Adum da Asafo. An koresu ba zato ba tsammani a ranar Alhamis din inda ka rufe shagunansu, kamar yadda jaridar Asenso Mensah ta ruwaito.

Jami'in hulda da jama'a na kungiyar, Albert Mensah Offei, ya sanar da gidan rediyon Joy FM cewa, nan ba da dadewa ba irin wannan hukuncin zai shafi sauran sassan kasar.

Hakazalika, kamar yadda Ghanaweb.com ta sanar, hukuncin kungiyar za a iya fassara shi da maida martani ga Najeriya akan rufe iyakokinta da tayi wanda hakan ya shafi 'yan kasuwar yankin kasashen Afirka ta yamma

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel