Ku dafawa Shugaba Buhari a samu a gyara Najeriya – Fayemi ga su Atiku

Ku dafawa Shugaba Buhari a samu a gyara Najeriya – Fayemi ga su Atiku

Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya yi kira na musamman ga Atiku Abubakar da cewa ya zo a hada hannu da juna tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin a gyara Najeriya.

Kayode Fayemi ya yi wannan kira ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai, Yinka Oyebode, wanda ya fitar da jawabi a madadinsa a Ranar Alhamis, 31 ga Watan Oktoba, 2019.

A jawabin da Mista Yinka Oyebode, ya fitar, ya nemi ‘dan takarar shugaban kasar na PDP da sauran ‘yan hamayya su zo a hadu da shugaba Muhammadu Buhari domin ganin an ci da kasa.

Gwamna Fayemi ya fitar da wannan jawabi ne dazu a Garin Ado Ekiti bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a game da zaben 2019 inda aka tabbatar da nasarar da INEC ta ba shugaban kasar.

KU KARANTA: 2019: Ka dawo Jam'iyyar APC kawai - Tinubu ga Atiku

Dr. Fayemi yake cewa: “Wannan ya yi daidai ga tsarinmu. Wannan nasara ce ga damukaradiyya. Nasarar ba ta APC ce kurum ba. Nasara ce ga duk wani mai nufin kasar mu Najeriya da alheri.”

“Jama’a sun yi magana kuma kotu sun tabbatar da burin su. A madadin gwamnati da mutanen jihar Ekiti, ina taya shugaban mu Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo…

“…da jam’iyyar APC da kuma sauran al’ummar kasa murnar wannan. Na yi imani cewa hukuncin babban kotun ya kawo karshen duk wani dauke hankali da ake samu daga korafin zaben 2019.

“Yayin da mu ke taya APC murna, mu na kira ga ‘yan hamayya su shiga tafiyar shugaban kasa wajen ganin an gyara Najeriya ta fuskar kawo cigaban zamantakewa da tattalin arziki.” Inji sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel