Pantami ya bayyana irin shirin da ma'aikatarsa ke yi wa matasan da suka kammala karatu

Pantami ya bayyana irin shirin da ma'aikatarsa ke yi wa matasan da suka kammala karatu

Ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya ce ma'aikatarsa tana aiki tukuru wajen ganin ta ilimantar da matasan da suka kammala karatu a kan hanyoyin da zasu dogara da kansu.

Pantami ya ce ya kamata matasan su kasance masu tunanin daukan wasu aiki, sabanin suke zaman jiran a basu aiki bayan sun kammala karatu.

Ministan ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Uwa Suleiman, wanda ya wakilce shi a wurin taron gidauniyar kamfanin sadarwa na MTN wanda aka yi ranar Alhamis a Abuja.

A cewar ministan, za a karkatar da akalar ilimi zuwa koyar da matasa dabarun koyon sana'o'i daban-daban ta hanyar sarrafa bahanai a fasahance (ICT).

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Atiku ya fadi su waye suka lalata bangaren shari'a

"Manufar ilimi a wannan zamani ita ce yaye daliban da zasu dauki wasu aiki, ba wadanda zasu zauna jiran a dauke aiki ba. Hakan shine burin ministan sadarwa," a cewarsa.

Pantami ya bayyana cewa matasan da suka kammala karatu zasu samu horo da ilimin sanin harkokin da zasu basu damar rike kansu har su dauki nauyin wasu.

Pantami ya jinjina wa MTN tare da yaba wa kokarinsu na taimakon jama'a, musamman bayar da tallafin karatu ga dalibai masu kwazo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel