Za a tura hazikan Yara ketare domin Digiri da Digirgir da Digir-Digir

Za a tura hazikan Yara ketare domin Digiri da Digirgir da Digir-Digir

Mun samu labari cewa Ministan harkar ilmi a Najeriya, Malam Adamu Adamu, ya sanar da cewa an bude shafin da za ayi rajistar yin jarrabawar CBT ta fita kasashen waje domin yin karatu.

Kamar yadda Ministan ya bayyana a Ranar Laraba 30 ga Watan Oktoba a Garin Abuja, za a fitar da zakakuran masu neman karatun Digiri da Digiri na biyu da na uku na MSc da PhD a wannan tsari.

Gwamnatin tarayya ta kan dauki nauyin Daliban da su ka kammala karatun Sakandare da takardu masu kyau ko kuma Digiri ga masu bidar zuwa kasashen wajen domin Msc da PhD.

Kasashe goma sha biyu na Nahiyar Asiya, Amurka, Afrika da kuma Turai da za a tura wadanda su ke son yin Digiri na farko a ketare sun hada kasar Rasha, Morocco, Aljeriya, da kuma Sabiya.

KU KARANTA: Wani Shugaban Afrika ya ce wani abu game da rufe iyakokin Najeriya

Har ila yau gwamnatin Najeriya za ta dauki dawainiyar wadanda su ke da burin karatu a kasashen Hungari, Masar, Tunisiya, Turkiyya ko kumaJafan, Romaniya, Kuba ko Macedoniya.

Haka zalika akwai damar da aka warewa wadanda su ka kammala Digirin farko, su ke da niyyar zarcewa zuwa Digiri na biyu zuwa kasashe irin Hungary, Turkiyya, Jafan, da kuma kasar Mexico.

Wadanda su ke sha’awar karanta ilmin fasaha, harkar gona, kimiyya, lissafi, harshe, wasanni, da kuma shari’a, kuma su ka ci wannan jarrabawa ne kadai za su samu wannan damar fita kasashen.

Masu Digirin farko a jami'o'in Rasha za su iya komawa domin su yi Digirgir. Kasar Koriya ta Kudu ta na cikin kasashen. Sannan akwai kaso marasa yawa da aka warewa masu karatun Likita.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel