Jam'iyyar APC ta zargi jami'an 'yan sanda da tarwatsa musu taro a Zamfara

Jam'iyyar APC ta zargi jami'an 'yan sanda da tarwatsa musu taro a Zamfara

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa jami'an 'yan sanda sun tarwatsa musu taron su da suke gudanarwa a wasu kananan hukumomi a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban jam'iyyar na jihar, Lawal Liman ne ya yi wannan zargin a hirar da aka yi da shi a ranar Alhamis a Gusa.

Ya ce, "Ka san mun yi taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar mu a kananan hukumomi 14 na jihar nan a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Mutuwar Al-Baghdadi: Kungiyar ISIS ta yi sabon shugaba

"Abin takaici mun samu rahotannin cewa wasu jami'an 'yan sanda sun hana 'yan APC da magoya bayansu amfani da damar da doka ta ba su."

Sai dai mai magana da yawun 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu ya ce an hana su yin taron ne sakamakon dokar da aka kafa a jihar na hana taron siyasa, da gangami da tattaki.

Mista Shehu ya ce a ranar 24 ga watan Satumba rundunar 'yan sanda a jihar ta saka dokar hana taron siyasa, gangami da tattaki don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

Ya ce dokar da rundunar ta kafa ba ta da alaka da siyasa sai dai an kafa ta ne don amfanin al'ummar jihar kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel