'Yan Hisba sun kama karuwai 93 a Kano, 23 cikinsu na dauke da cutar HIV

'Yan Hisba sun kama karuwai 93 a Kano, 23 cikinsu na dauke da cutar HIV

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama mutane 93 da ake zargin karuwai ne kuma 23 cikinsu suna dauke da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

Kwamandan hukumar na jihar, Sheikh Muhammad ibn-Sina ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis.

Ya ce jami'an hukumar sun kai samame a Badume Joint a karamar hukumar Bichi a jihar inda ya yi kaurin suna a matsayin matattaran karuwai da wasu masu aikata laifi.

Sheikh Sina ya ce, "Cikin wadanda muka kama 23 mata da maza hudu, gwajin da likita ya yi ya nuna suna dauke da cuta mai karya garkuwar jiki da HIV."

DUBA WANNAN: Tirkashi: Wani dan majalisar Najeriya ya ciri tuta, ya nada hadimai 36

Ya ce an gudanar da sumamen ne don tsaftace jihar kamar yadda ya ke cikin dokar jihar da ta hana karuwanci da sauran ayyukan masha'a.

Ya kara da cewa rundunar ta Hisbah za ta cigaba da ya ki da dukkan ayyukan da ka iya gurbata tarbiyar al'umma jihar a duk inda ake aikata shi.

A wani rahoton kuma mun kawo muku cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kafa kwamitin bincike mai dauke da mutum 16 don bin didigin yadda aka sace wasu yara 9 'yan Kano aka kai su jihar Anambra.

Rundunar 'yan sanda sun kama wasu mutane da ake zargi da hannu wurin safarar kananan yaran zuwa jihohin na Kudu.

Baya ga yara taran na farko, 'Yan sanda sun kuma sake ceto wasu kananan yaran biyu a hannun wasu masu safarar kananan yaran a jihar ta Anambra.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel