Ballon D’Or: ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo zai samu nasara a 2019

Ballon D’Or: ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo zai samu nasara a 2019

- Cristiano Ronaldo ake hasashen zai dauki kofin Ballon d’Or na bana

- ‘Dan wasan mai shekaru 34 yana kokarin tserewa Abokin adawa Messi

- Gwarazan Duniya Messi da Ronaldo duk su na da kofin Ballon d'Or biyar

Cristiano Ronaldo ne ‘dan kwallon da ake sa ran cewa zai lashe kyautar Ballon d’Or na wannan shekarar. Rahotanni daga kasar Italiya su na yawo cewa ‘Dan wasanna Juventus ne zai yi nasara.

Ronaldo ya na tare ne da Lionel Messi da kuma ‘dan wasan baya, Virgil van Dijk a jerin wadanda ka iya samun wannan babbar kyauta ta kwallon kafa. Yanzu Ronaldo ya tserewa sa’annin na sa.

Jaridar Corriere dello Sport ta ce Ronaldo ya na daf da cin Ballon d’Or na shida kenan a tarihinsa. Tsohon ‘dan wasan na Real Madrid da kuma Lionel Messi sun ci wannan kyauta sau biyar a baya.

KU KARANTA: Ronaldo bai da sa'a a Duniya a wajen sanin raga - Messi

Wannan jarida ta kasar waje ta ce alamu sun nuna cewa Ronaldo zai yi wa Abokin adawa, Messi na kungiyar Barcelona gaba a karshen wannan shekara. A cikin Disamba za a bada kyautar.

Ronaldo ya yi wata hira da gidan kwallon kafar Faransan inda ya yi maganar yiwuwar cin kyautar bana. ‘Dan wasan ya yi gum game da damar da Messi da Van Dijk su ke da ita wannan karo.

Ana tunanin cewa an tsakuro wani bangare kadan ne daga cikin hirar da aka yi ne Tauraron ‘dan wasan kwanakin baya. A shekarar nan ne dai Messi ya zama gwarzon kwallon shekara na FIFA.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel