Yanzu-yanzu: Dokar kisa ga masu garkuwa da mutane a Kano

Yanzu-yanzu: Dokar kisa ga masu garkuwa da mutane a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya umurci ma'aikatar shari'ar jihar ta gyara dokar jihar kan masu garkuwa da mutane zuwa hukuncin kisa.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron rantsar da kwamitin binciken yaran Kano tara da aka sace kuma aka sayar da su a Onitsha, jihar Anambara.

A cewarsa, ya baiwa hukumar kwanaki 30 du kammala bincikensu kuma su kawowa gwamnan sakamako.

Ya siffanta garkuwa da mutane matsayin babban laifi da ya saba dukkan addinai.

DUBA WANNAN An fara farautar masu tabin hankali a jihar Sokoto

Idana bazamu manta ba, a cikin watan da ya gabata ne aka samo yara 9 daga jihar Anambra wadanda aka sace a Kano kuma aka canza musu sunaye da addini.

Hakan kuwa ya jawo hankulan hukumomi, shuwagabanni da mutane masu fada aji.

A hakanne kuwa gwamnatin jihar Kano da ta tarayya suka yi alkawarin yi wa yaran adalci.

Cibiyar binciken cin zarafi ta jihar Kano ta gano cewa daya daga cikin yara 9 da aka sace anyi mata fyade so da yawa.

Shugaban cibiyar, Nasiru Garko, ya bayyana hakan ga jaridar Kano Focus bayan dubawar da aka yiwa yarinyar mai shekaru 10 kacal a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel