An fara farautar masu tabin hankali a jihar Sokoto

An fara farautar masu tabin hankali a jihar Sokoto

Gwamnatin jihar Sokoto ta fara farautar matasan jihar da ke fama da jarabawan tabin hankali da hauka domin yi musu jinya har su samu lafiya, wakilin gwamnatin ya laburta

Hukumar zakka da wakafi ta fara samame da kama mahaukatan da ke cikin garin inda ake kai su Asibitin tarayya ta masu rashin lafiyar tabin hankali da ke garin Kware.

Shugaban hukumar zakka da wakafi, Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), ya ce za'a kwantar da marasa lafiyar ne har su ji sauki, kuma hukumar ce za ta dauki nauyin cin su da maganin su har su samu sauki, idan an sallame su, za a hada musu da wani abu dan dogaro da kai.

KU KARANTA: Akalla mutane 65 sun hallaka yayinda tukunyar gas ya fashe cikin jirgi

"Kowane mutum ana kashe mai naira 48,000 a kowane wata a asibitin Kware idan an kwantar da shi.

"A jiya kadai an kai mutum 13, maza da mata. Hukumar Hizba da ta Civil Defence na cikin wadanda suka kama aiki", cewar Maidoki.

A karshe Shugaban ya yi kira ga masu hannu da shuni da su shigo cikin shirin dan taimakawa al'umma, maimakon barin gwamnati kadai da aikin.

A bangare guda, A ranar Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman, a Riyadh, babbar birnin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin Najeriya ta bada rahoton cewa ganawar na cikin tattaunawar da shugaba Buhari zai yi kafin tafiya Makkah a yau ta babbar filin jirgin saman sarki Abdulaziz a Jeddah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel