Waiwaye: Martanin Buhari bayan kotun koli ta yi watsi da karar da ya daukaka a an zaben 2011

Waiwaye: Martanin Buhari bayan kotun koli ta yi watsi da karar da ya daukaka a an zaben 2011

A ranar Laraba ne kotun koli ta yi watsi da karar da Atiku da jam'iyyar PDP suka daukaka zuwa kotun koli bayan kotu sauraron korafin zabe ta farko ta yi watsi da kalubalantar nasarar shugaba Buhari a zaben shugaban kasa na 2019 da suke yi.

Kotun kolin bata wani bata lokaci ba wajen yin watsi da karar Atiku da PDP suka daukaka, kamar dai yadda kotun farko ta tabbatar wa da shugaba Buhari nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar a farkon shekarar 2019.

Har yanzu ana cigaba da bayyana ra'ayi tare da tofa albarkacin baki a kan hukuncin da kotun kolin ta zartar ranar Laraba.

Tuni Atiku da jam'iyyar PDP suka nuna rashin gamsuwarsu a kan hukuncin da kotun ta zartar, lamarin da yasa suka bukaci kotun ta bayyana dalilanta na yanke hukuncin da ta zartar.

An yi irin wannan cacar baki da musayar yawu a lokacin da kotun koli ta yi watsi da karar da shugaba Buhari ya shigar a lokutan da ya yi takarar shugaban kasa a shekarar 2003, 2007 da kuma 2011.

"Kamar yadda ta faru a shekarar 2003 da 2007, kotun koli ta yi watsi da ikirarin jam'iyyar CPC a kan cewa an tafka magudi a zaben 2011, kotu ta ce an gudanar da zabe kamar yadda ya kamata. Duk wanda ya shaida yadda aka gudanar da zaben 2011 ya san cewa akwai siyasa a cikin wannan hukunci da kotun koli ta zartar," a cewar Buhari, yayin da yake gana wa da manema labarai jim kadan bayan kotun koli ta tabbatar wa da shugaba Goodluck Jonathan nasarar da ya samu.

DUBA WANNAN: Da tuni an barke da murna a fadin Najeriya da kotun koli ta sauke Buhari - Buba Galadima

Buhari ya cigaba da cewa, "wannan kotun kolin bata da maraba da kotun koli ta shekarar 2003 da 2007. Bari na yi muku tuni a kan abinda ya faru a baya, mun kalubalanci hukumar zabe ta gabatar da sakamakon zaben 2003 a gaban kotu, amma duk da sun gaza yin hakan, kotu ta tabbatar da sahihancin zabe.

"Haka ta kasance a shekarar 2007, kotu ta yi watsi da karar da muka shigar duk da irin manyan hujjojin da muka gabatar a gabanta a kan yadda aka tafka magudi a zaben shugaban kasa.

"To duk wadannan nafila ne idan aka kwatanta su da hukuncin da kotun koli ta yanke a shekarar 2011. Mun yi tunanin za a samu canji a hukuncin da kotu zata zartar saboda an samu sabon shugaban INEC, Farfesa Attahiru, mutumin da ake ganin mai gaskiya ne. Mu bamu ga gaskiyarsa da ake magana ba, saboda ya karbi kudi a hannun gwamnati kusan biliyan N100 domin shirya sahihin zabe, amma haka aka tafka magudi a fadin Najeriya, mun san cewa ba a gudanar da zabe bisa ka'aida ba a jihohi a kalla 25 daga cikin 36, mun sanar da kotu, mun gabatar da shaidu, amma kotu ta kawar da kanta daga dukkan shaidun da muka gabatar duk da INEC ta kasa kare kan ta. Su a wurinsu, akwai adalci a hukuncin da suka zartar duk da duniya ta sani kuma ta ga abinda ya faru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel