Katsina: An yi garkuwa da Mai dakin Mataimakin Akanta Janar

Katsina: An yi garkuwa da Mai dakin Mataimakin Akanta Janar

Labarai su na zuwa mana cewa an sace Matar mataimakin shugaban Akantan gwamnatin jihar Katsina. Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan a Ranar Alhamis, 31 ga Watan Oktoba, 2019.

Rahotannin sun ce wadannan ‘yan bindiga da ba a iya gane su ba, sun kutsa har cikin gidan jami’in gwamnatin ne su ka dauke Mai dakinsa, Hajiya Lubabatu Sani Lawal BK a Ranar Laraba.

Wannan mummunan abu ya faru ne a jiya da kimanin karfe 9:00 na dare a gidan Akantan da ke Unguwar GRA a cikin Garin Katsina. Ana zargin cewa ‘yan bindiga goma ne su ka shiga gidan.

Wani Bawan Allah da abin ya faru a gaban idanunsa ya bayyanawa Daily Trust cewa wadannan ‘yan bindiga sun zo ne a cikin motoci biyu wanda daga ciki akwai wata motor Peugeot kirar 206.

KU KARANTA: Dubun masu garkuwa da mutane ta cika a Jihar Kebbi

Majiyar ta ce sai da aka yi wa mutanen gidan ‘dan-karen duka kafin a lalubo Matar gidan. Bayan sun gano Amaryar ne su ka jefa ta cikin mota su ka yi gaba. Har ya yanzu dai babu labarin ta.

Lubabatu Sani Lawal ita ce Amaryar mataimakin Akanta Janar na jihar Katsina. Kamar yadda mu ka samu labari, kwananaki ta dawo aikin hajji daga kasa mai tsarki tare da wasu ‘ya ‘yan ta.

Shi ma dai Mai gidan na ta bai dade da samun karin matsayi zuwa mataimakin Akanta Janar na gwamnatin jihar Katsina ba. A baya shi ne shugaban ma’ajin jihar kafin ya samu wannan kujera.

Har yanzu dai jami’an tsaro ba su ce uffan game da wannan lamari ba. Babu alamun cewa wadannan mutane da ake zargin cewa masu garkuwa ne sun tuntubi Iyalin ta domin karbar kudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel