Gidan gyaran hali ne inda Nnamdi Kanu zai fi samun tsaro, inji mai Shari'a Nyako

Gidan gyaran hali ne inda Nnamdi Kanu zai fi samun tsaro, inji mai Shari'a Nyako

A ranar Alhamis, Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ya sanar da babban kotun tarayya da ke Abuja cewa, a shirye yake don fuskantar hukunci matukar kotun ta tabbatar masa da za ta bashi kariya.

Kanu ya sanar da mai shari'a Binta Nyako, ta bakin lauyansa, Ifeanyi Ejiofor.

Ejiofor ya sanar da kotun cewa, "Mun mika bukatar beli a ranar 1 ga watan Afirilu, 2019. Muna bukatar kotu da ta dawo da sharuddan belinsa amma da alkawarin bashi kariya idan ya dawo kasar nan don fuskantar shari'arsa," in ji shi.

A bangaren gwamnatin tarayya, Lauyan gwamnatin tarayya, Labaran Shu'aibu, ya sanar da kotun cewa yanzu ne yaga hakan, abinda yaci karo da bukatar belin.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

Shuaibu ya bukaci kotun da ta dage sauraron karar don bashi damar nazarin a kan sabon cigaban.

Yayin yanke hukunci, Jastis Nyako, wacce ta dage sauraron shari'ar zuwa 16 ga watan Janairu, ta ce, hanyar da kotu za ta tabbatar da tsaronsa shine ajiyeshi a gidan gyaran hali.

Ta ce, ko masu shari'a a kasar nan basu da tsaro cikakke.

"Ko masu shari'a a kasar na sacesu ake yi. Gidan yari ne kadai wajen da muke tunanin zai iya samun tsaro," in ji ta.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, Jastis Nyako ta bada belin Kanu saboda neman lafiya a ranar 25 ga watan Afirilu, 2017 kuma ta bukaci ya kawo tsayayyu uku.

Daya daga ciki ya kasance sanata, daya malamin addini sai kuma dayan ya kasance mutum mai daraja wanda ke da kadara a Abuja.

Mai shari'ar ta ja kunnen shugaban IPOB akan tattaunawa da manema labarai, yin tattaki ko kuma taron sama da mutane 10 yayin da aka bada belinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel