Gwamnatin tarayya ta aika ma yan gudun hijira takardar sallama daga wani sansani

Gwamnatin tarayya ta aika ma yan gudun hijira takardar sallama daga wani sansani

Tsuguni bata kare, yan gudun hijira daga wasu kauyukan jahar Filato dake tsugune a farfajiyar ofishin hukumar hakar albarkatun kasa, Nigerian Mining and Geosciences Society, NMGS, dake garin Jos sun sake fadawa wani mawuyacin hali.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito hukumar NMGS ce ta aika musu da takardar tashi daga harabar tasu cikin wata takarda dake dauke da kwanan watan 22 ga watan Oktoban 2019, tare da sa hannun shugaban hukumar, Dr A.S Olatunji.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin wani hamshakin mai taimakon jama’a a Katsina

Shugaban NMGS ya aika ma jami’in dake kula da sansanin yan gudun hijiran kwafin wasikar, tare da babban jami’in hukumar bada agaji ta Red Cross da kuma shugaban shugaban bada agajin gaggawa ta NEMA reshen jahar Filato.

NMGS tace dalilinta na tasan yan gudun hijiran shi ne domin ta gudanar da cikakken gyara ga ofishin nata daga ranar 31 ga watan Oktoban 2019 sakamakon lalacewa da gine ginen suka yi. “Don haka wannan shine gargadi na karshe, saboda dan kwangila zai fara aiki a wannan rana.” Inji ta.

Wani jami’in NMGS da bai bayyana sunansa ba ya tabbatar da takardar sallaman, sai dai yace hukumar na kokarin gyara sakatariyarta ne tare da kare shi daga lalacewa, ya kara da cewa ai idan ba’a yaba musu ba, toh ba za’a zagesu ba, saboda su kadai suka iya baiwa yan gudun hijirar mafaka.

A nasa bangaren, kwamishinan watsa labaru na jahar Filato, Dan Manjang ya tabbatar da lamarin, sa’annan ya roki NMGS ta kara tausaya ma yan gudun hijira, tare da daga musu kafa zuwa wani lokaci sakamakon gwamnati na kokarin nema musu sabon sansani.

Adadin mutanen da suka nemi mafaka a sakatariyar NMGS ya haura 4,000, kuma yawancinsu sun fito ne daga kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom a sanadiyyar hare haren yan bindiga, a yanzu dai bai wuce mutane 300 suka rage ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel