Buba Galadima ya fadi halin da 'yan Najeriya zasu shiga da Atiku ya samu nasara a kotun koli

Buba Galadima ya fadi halin da 'yan Najeriya zasu shiga da Atiku ya samu nasara a kotun koli

Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Buba Galadima, yace da yanzu 'yan Najeriya sun kaure da murna da kotun koli ta sauke shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba.

Kotun koli a ranar Laraba tayi watsi da daukaka karar da PDP da dan takararta, Atiku Abubakar suka yi akan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ya tabbatar da nasara a zaben watan Fabrairu na 2019. Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Atiku ya fadi su waye suka lalata bangaren shari'a

A yayin zantawar da yayi da gidan talabijin din Channels a ranar laraba, Galadima yace, "Idan da ace hukuncin yau yasa an sauke Buhari daga kujerarsa, na tabbata da yanzu 'yan Najeriya sun kaure da murna da farinciki a fadin kasar nan,"

"Da yanzu mutane na ta murna tare da farinciki kuma suna watsa ruwa a tituna. Amma ko kunga mutanen da suka yi murna akan wannan hukuncin?" ya tambaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel