'Yan Najeriya su na cin gurbataccen shinkafa - Hameed Ali

'Yan Najeriya su na cin gurbataccen shinkafa - Hameed Ali

- Shugaban kwastam, Col. Hameed Ali ya bayyana cewa, 'yan Najeriya na cin shinkafa lalatacciya da aka shigo da ita daga kasashen ketare

- Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji shinkafar kasashen ketaren don 'yan kasuwa sun canza musu buhunhuna ta yadda baza su gane ba

- Ya jaddada cewa, ba gudu ba ja da baya, hukumar kwastam din sai ta hana shigo da kayan 'sumogal' cikin kasar nan

Shugaban hukumar kwastam ta kasa, Col. Hameed Ali mai murabus, ya ce, 'yan Najeriya na cin shinkafar kasashen waje wacce ta lalace.

Col. Ali, wanda ya sanar da hakan a ranar Laraba ga hukumar kwastam reshen jihar Ribas, ya ce wadanda suka kawo lalatacciyar shinkafar cikin kasar nan sun canza mata buhunhuna ne sannan suke siyarwa da 'yan kasa.

Ya ce, kayan 'sumogal' da ake shigo da su kasar nan duk ana haka ne don durkusar da hukumar. wanda ya tabbatar da za ta shawo kan kalubalen.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

"Muna cin lalatacciyar shinkafa. Idan ta kawo cutar daji sai mu fara neman wanda zamu dorawa laifi. Duk kayayyakin da suke shigowa dasu suna yin hakan ne don durkusar da hukumarmu, amma tabbas zamu shawo kan hakan."

"Dole ne mu sanar da 'yan Najeriya mummunar illar cin kayayyakin. Ina kara jaddadawa, zamu yi duk abinda zamu iya don ganin mun hana shigo da kayan," inji Ali.

Col. Hameed Ali, ya Cuba kwantainoni 98 da ke kunshe da tumatir, shinkafa, man gyada, tayel, karafuna da sauransu da zasu kai kimanin naira biliyan daya a filin jiragen ruwa na Fatakwal da Onne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel