Dalilin da ya sa muke kawance da kasar Rasha - Buhari

Dalilin da ya sa muke kawance da kasar Rasha - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya ce Najeriya tana kawance da kasar Rasha ne don ta na 'taimaka wa' Najeriya a bangarorin da gwamnati ta bawa muhimmanci da suka hada da tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa.

Buhari ya yi wannan furucin na yayin amsa wata tambaya da aka masa a rana ta biyu na tattaron tattalin arziki da saka hannun jari a aka gudanar a Riyadh inda aka tambaye shi ko Rasha yanzu ita ce babbar kawar Afirka.

Shugaba Muhammadu Buhari ya hadu da takwarorinsa Shugaba Mahamadou Issoufou na kasar Nijar da Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya yayin zaman tattauna don cimma matsaya kan hanyoyin da za a inganta kasuwanci da saka hannun jari a Afirka.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

Ya mika godiyarsa ga kasar Rasha don cigaba da kasancewa abokiyar tafiya wurin cigaba a Najeriya har ma ya ambaci taimakon da ta yi wa kasar yayin yakin basasar da ya faru a baya.

"Dukkan wadanda suke nazarin cigaban kasashe masu tasowa za su iya ganin irin abubuwan da Rasha ta yi mana duk lokacin tana Kungiyar Soviet. Ba za mu taba manta taimakon da ta yi mana ba yayin yakin basasa a siyasance da kuma a bangaren tattalin arziki. Kasar Rasha ta taimakawa Najeriya a hanyoyi daban-daban," inji shugaba Buhari cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Shehu Garba ya fitar.

Shugaban na Najeriya ya ce sabbin sauye-sauyen da aka yi a fannin aikin noma shine tsarin da zai fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga kancin talauci cikin shekaru 10 masu zuwa. Ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an cimma wannan burin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel