Aikin cigaba: Gwamnati za ta sanya wutar Solar a gidajen jahar Kaduna

Aikin cigaba: Gwamnati za ta sanya wutar Solar a gidajen jahar Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana shirinta na sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a wasu gidaje guda 3, 400 a wasu kananan jahohin jahar guda uku, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin ta ware makudan kudi naira biliyan 8.3 domin gudanar da wannan gagarumin aiki a kananan hukumomin Kubau, Jema’a da kuma Kajuru a shekarar 2020.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin wani hamshakin mai taimakon jama’a a Katsina

Shugabar hukumar samar da wutar lantarki ta jahar Kaduna, Dapola Papoola ce ta bayyana haka yayin da ta gurfana a gaban majalisar dokokin jahar Kaduna domin ta kare kasafin kudin hukumarta a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba.

Papoola ta bayyana cewa baya ga sanya wuta a gidaje 3400, gwamnatin Kaduna ta sanya aikin samar da wutar Solar mai tsawon kilomita 2 a dukkanin mazabun siyasar jahar Kaduna guda 255, a cikin kasafin kudinta na shekarar 2020.

Bugu da kari, Papoola ta bayyana ma yan majalisar cewa gwamnati za ta sanya wutar solar a hukumar samar da ruwan sha na Zaria da na Malali domin da haka ne kadai za’a tabbatar da suna aiki awanni 24 tare da samar da ruwan shag a jama’a.

A hannu guda kuma, shugaban hukumar kula titunan jahar Kaduna, KADRA, Mohammed Magaji ya bayyana cewa hukumarsa ta ware naira biliyan 31 a kasafin kudin 2020 domin gudanar da wasu manyan ayyuka a jahar Kaduna.

Daga cikin manyan ayyukan akwai ginin sabon gadar sama a Kawo. Sai dai Magaji ya shaida ma majalisar cewa aikin KADRA ya shafi iya karamar hukumar Kaduna ta kudu, Kaduna ta Arewa, Igabi da kuma Chikun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel