Daga kasar Amurka: Shaida zai tabbatar wa da kotu laifin tsohon gwamnan PDP a arewa

Daga kasar Amurka: Shaida zai tabbatar wa da kotu laifin tsohon gwamnan PDP a arewa

Babban kotun tarayya ta Abuja a ranar Laraba, ta mika bukata ga hukumar yaki da rashawa ta EFCC da ta karba shaidar wani ta bidiyo da zai gabatar. Jastis Okon Abang, wanda ya bada umarnin, ya dage sauraron shari'ar zuwa 5 ga watan Nuwamba na wannan shekarar.

A ranar Talata ne mai shari'ar ya dakatar da sauraron shari'ar zuwa washegari.

Lauyan EFCC, Rotimi Jacob, SAN, ya bukaci kotun da ta amince da sauraron wani Kobis ta bidiyo a yanar gizo don zai bada shaida ne akan zargin almundahanar naira biliyan 40 da ake wa tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da wasu.

Yayin yanke hukunci akan bukatar masu kara, mai shari'ar yace an miko wannan bukatar ne a ranar 29 ga watan Oktob a. Yace a halin yanzu, masu karar sun kawo shaidu 20 ga kotun. Ya lissafo dage-dagen da aka dinga yi akan lamarin.

"An dage sauraron shari'ar a zuwa ranar 29 ga watan Oktoba ne wadanda ke karar su samu damar kawo shaidarsu ta karshe" in ji shi.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Atiku ya fadi su waye suka lalata bangaren shari'a

Mai shari'ar, ya ce, lauyan EFCC, Rotimi Jacob, ya kasa kawo shaida ta wajen Kobis, wanda shine tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa a wancan lokaci. Jacob ya sanar cewa, Kobis ba zai iya zuwa Najeriya ba saboda matsalar lafiya da yake fama da ita wacce tasa yake zama a Amurka yanzu.

Jacob ya bukaci kotun da ta ba shi damar karbar shaida daga Kobis ta bidiyo kamar yadda sashi na 232, sakin layi na 3 na dokokin ACJA ta gindaya. Ya kara da cewa, Kobis ya ki zuwa Najeriya ne saboda hakan zai iya zama barazana ga rayuwarsa.

Ya kara da cewa, wani ma'aikacin banki ya rasa ransa a wannan shari'ar.

Duk da alkalin yace, massu kare kansu a shari'ar sun soki wannan salon shaidar don ganin cewa babu kwakwarar shaida da ta nuna cewa rayuwar shaidar na cikin hadari.

Mai shari'ar da ya saurari dukkan bangarorin, yace a cikin abubuwan da suka fada akwai ababen duba. Ya yanke cewa, kotun bazata ga laifin masu kara ba da suka kasa kawo shaidarsu haka kuma bazata ga laifin masu kare kansu ba.

"Shaidar na amfani da damar cewa bamu da karfin shari'a a kanshi tunda yana Ingila," in ji Abang. Ya bayyana cewa dole ne ayi adalci ba tare da an dubi yadda aka samu shaidar ba. A don haka ne ya aminta da bukatar masu karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel