Yaki dan zamba: Gwamna El-Rufai ya fara yakin neman zaben shugaban kasa

Yaki dan zamba: Gwamna El-Rufai ya fara yakin neman zaben shugaban kasa

Wata kungiyar magoya bayan gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai mai suna Nasirriya sun bude wani ofishin yakin neman zaben El-Rufai a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023 a garin Jos na jahar Filato.

Jaridar BluePrint ta ruwaito shugaban Nasiriyya, Hajiya Nafisatu Omar ta bayyana cewa El-Rufai ya cancanci zama shugaban kasar Najeriya saboda mutum ne da baya nuna bambamcin addini ko kabilanci.

KU KARANTA: Ajali ya yi kira: Tsohon gwamnan jahar Legas ya mutu

Yaki dan zamba: Gwamna El-Rufai ya fara yakin neman zaben shugaban kasa

Fastan yakin neman zaben
Source: Facebook

Nafisatu ta bayyana haka ne a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba yayin taron bude ofishin goyon bayan El-Rufai a garin Jos, da kuma rantsar da ita a matsayin jagorar kungiyar, tare da sauran masu rike da mukamai a kungiyar.

“Malam Nasir El-Rufai ne kadai mutumin da yafi cancanta ya zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023 saboda shi ba barawo bane, bashi da halin cin hanci da rashawa, bashi da tsatstsauran ra’ayin addini, kuma baya kabilanci kamar yadda za’a gani a yadda yake tafiyar da gwamnatin Kaduna.” Inji ta.

Shi ma shugaban Nasiriyya na kasa, Alhaji Ibrahim Babuga Garkuwan Rijau ya bayyana cewa sun fara sanya tubalin yakin neman zaben shugabancin kasa na El-Rufai ne tun yanzu domin tabbatar da samun nasara a 2023.

“Ai bamu fara wannan shiri da wuri ba, duba da cewa tuni mutanen Legas suka fara yin kiraye kiraye ga Malam Nasiru ya fito takarar shugaban kasa, toh me zai hana mu yi irin haka a nan?” Inji Rijau wanda shi ne mataimakin shugaban APC na yankin Arewa maso yamma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel