An jefa kan alade a wani sabon Masallacin Juma'a da ake ginawa

An jefa kan alade a wani sabon Masallacin Juma'a da ake ginawa

- A kasar Jamus an jefa kan alade a wani sabon Masallacin Juma'a da ake ginawa

- Har yanzu dai ba a san ko wanene ya jefa wannan kan aladen ba cikin masallacin duk da an sanarwa da hukumar 'yan sandan yankin

- Yanzu dai an bayyana cewa gwamnatin garin da kuma kwamitin Masallacin suna aiki tare saboda wannan hari da aka kai

A kasar Jamus an jefa kan alade a wani sabon Masallacin Juma'a da ake gina a garin Schwelm dake yankin jihar Ren Vestafalya ta arewa.

Wani mutumi da har zuwa yanzu ba a san kowanene ba ya jefa kan alade a wani babban Masallacin Juma'a da kungiyar hadin kan Musulunci ta Diyanet ta Turkiyya ke ginawa a garin Schwelm, inda bayan ma'aikatan wajen sun ga wannan kan alade sai suka sanar da jami'an tsaron wajen.

Yanzu haka dai shugabannin wannan Masallaci sun mika korafinsu ga hukumar 'yan sanda ta wannan yankin.

KU KARANTA: Wurin party ya rincabe da jini yayin da wasu samari 'yan gida daya suka yiwa abokinsu yankan rago a Kaduna

A sanarwar da manyan Masallacin suka fitar sun bayyana cewa wannan Masallaci da suke ginawa zai kara haskaka garin na Schwelm, sannan kuma sunyi Allah wadai da wannan hari, haka kuma Musulman garin da ma wadanda ba Musulmi ba na yankin sun nuna bacin ransu akan wannan abu da ya faru.

Yanzu dai an bayyana cewa gwamnatin garin da kuma kwamitin Masallacin suna aiki tare saboda wannan hari da aka kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel