Wurin party ya rincabe da jini yayin da wasu samari 'yan gida daya suka yiwa abokinsu yankan rago a Kaduna

Wurin party ya rincabe da jini yayin da wasu samari 'yan gida daya suka yiwa abokinsu yankan rago a Kaduna

- An kama wasu samari 'yan gida daya da laifin cakawa wani abokinsu wuka suka kar shi har lahira

- Samarin dai yanzu haka sun shiga hannu, inda alkali ya bayar da umarnin tsare su har zuwa lokacin da zai waiwayo kan su

- Wannan lamari dai ya faru a wajen wani biki da samarin suke yi a cikin birnin Kaduna

Wasu samari 'yan gida daya sun sanya kansu a cikin wani tashin hankali bayan an kama su da laifin amfani da wuka suka kashe abokinsu a wajen wani shagalin biki.

Alkalin kotun majistire ta jihar Kaduna, a jiya Laraba ya bada umarnin tsare wasu samari guda biyu da aka kama su da laifin kashe wani abokinsu.

Samarin masu suna Shawal Mohammed da kuma Anas Mohammed, sune 'yan uwan junan da aka kama su da laifin kashe wannan aboki na su.

Duka samarin suna zaune a unguwar Badarawa ne a cikin jihar Kaduna.

Alkalin kotun, majistire Lukman Sidi, yaki yadda da rokon da masu laifin suke yi masa, inda ya umarci jami'an 'yan sanda da su kai wannan rahoto na su zuwa ga babban darakta na yanke manyan hukunci.

Insp. Chidi Leo dan sandan da ya gurfanar da masu laifin ya bayyana cewa; "wani mutumi ne mai suna Shamsudeen Umar daga Kawo ya gabatar da wannan kara a ofishin 'yan sanda na Gabasawa, inda shi kuma DPO na ofishin 'yan sandan ya bada umarnin a mika su zuwa ga babbar helkwatar binciken manyan laifuka ta Kaduna a ranar 30 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Wannan abin kunya da yawa yake: Bidiyon wata mata ta hada kai da 'ya'yanta sun yiwa ubansu dukan tsiya saboda ya cinye musu abinci a gida

"Haka kuma a ranar dai da misalin karfe 1 na rana, wadanda ake zargin suka sake yin fada da wani mai suna Mubarak Sani dake Yantaba Road, Ungwan Shanu Kaduna a lokacin da suke biki.

"A lokacin da suke rikicin, wadanda ake zargin sunyi amfani da wuka suka kafa masa a wuya, inda ya samu mummunan rauni.

"An yi gaggawar garzayawa da shi babban asibitin koyarwa na Barau Dikko dake Kaduna, amma likitocin sun bayyana cewa ya mutu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel