Hukuncin kotun koli: Atiku ya fadi su waye suka lalata bangaren shari'a

Hukuncin kotun koli: Atiku ya fadi su waye suka lalata bangaren shari'a

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugabancin kasa na 2019, Atiku Abubakar, ya kwatanta hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Laraba da babban kalubalen da damokaradiyya ke fuskanta a kasar nan.

Idan zamu tuna, kotun kolin a ranar Laraba ta yi watsi da daukaka karar da Atiku da jam'iyyarsa suka yi suna kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugabancin kasa na 2019.

Yayin yanke hukuncin a ranar Laraba, shugaban alkalan Najeriya, Jastis Tanko Muhammad, wanda ya jagoranci sauran alkalai 6, yace, bayan duba da duk takardu da kuma shaidu akan shari'ar, an gano daukaka karar bata da amfani.

Amma kuma a takardar da ya fitar a ranar Laraba, Atiku ya zargi fannin shari'ar kasar nan da lalacewa tare da durkushewa sakamakon umarnin wasu tsirarun mutane da ke juya akalar siyasar kasar nan. Sune kuma suka warware duk wata cigaban damokaradiyyar da jam'iyyar PDP da mulkinta suka raina cikin shekaru 16.

DUBA WANNAN: SERAP ta rubuta wa Trump wasikar neman ya haramta wa gwamnoni 7 shiga Amurka

Takardar ta kunsa kalamai kamar haka: "An ce kotun kolin ce ta karshe saboda bata kuskure, bata kuskure saboda itace ta karshe. Na yarda cewa Ubangiji ne kadai baya kuskure a ko ina. Kuma 'yan Najeriya ne kadai basu kuskure a damokaradiyyarmu. Dole in rungumi hukuncin hanyar shari'ar da na zaba don bi,"

"Ko anyi adalci, ya rage ga 'yan Najeriya su yanke hukunci. A matsayina na mai bin damokaradiyya, na yi yaki don mutanen Najeriya. Zan kuma cigaba da yaki akan 'yan Najeriya, damokaradiyya da kuma adalci," in ji Atiku.

"Ina godiya ga 'yan Najeriya da suka jure tun farkon shari'ar nan har karshenta. Hukuncin nan yana daga cikin kalubalen damokaradiyya da dole mu fuskanta a kasar nan. fannin shari'ar kasar nan ya lalace tare da durkushewa sakamakon umarnin wasu tsirarun mutane da ke juya akalar siyasar kasar nan. Sune kuma suka warware duk wata cigaban damokaradiyyar da jam'iyyar PDP da mulkinta suka raina cikin shekaru 16."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel