Boko Haram ta kai ma Sojoji samame, ta halaka jami’ai 12

Boko Haram ta kai ma Sojoji samame, ta halaka jami’ai 12

Ma’aikatar tsaro ta kasar Nijar ta bayyana cewa Sojoji 12 ne suka gamu da ajalinsu yayin da gungun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka kai musu farmaki a wani sansanin Sojoji dake yankin Diffa na kasar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito sanarwa daga ma’aikatar tsaron kasar Nijar ta bayyana cewa a daidai lokacin fitowar alfijir ne yan bindigan suka kaddamar da harin, inda baya ga Sojojin da suka kashe, sun jikkata wasu guda 8.

KU KARANTA:Ya kamata Atiku da PDP su rungumi kaddara - Sanata Ahmad Lawan

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta’addan sun kai harin ne a sansanin Soji na Blabrine, inda zuwa yanzu bincike ya tabbatar da mutuwar Sojoji 12, 8 sun jikkata, sa’annan kuma an tabbatar mayakan Boko Haram dake biyayya ga jagorancin Abubakar Shekau ne suka yi wannan ta’adi.

Shi dai sansanin Blabrine bai wuce nisan kilomita 20 zuwa garin Diffa ba, haka zalika akwai tarin yan gudun hijira dake neman mafaka a garin Diffa wanda adadinsu ya kai mutum 230,000 da rikicin Boko Haram daidaita.

Kididdigan majalisar dinkin duniya,UN, ne ya tabbatar da wannan alkalumma, yayin da kuma ambaliyan ruwan sama daga rafin Komaudougou Yobe ta tafka ma yan gudun hijiran barna, inda ya tashi sama da mutane 40,000.

A yan kwanakin nan dai kumgiyar ta’addanci ta ISIS ta sha bayyana cewa mayakanta na ISWAP ne ke kai hare haren ta’addanci a yankin Diffa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel