SERAP ta rubuta wa Trump wasikar neman ya haramta wa gwamnoni 7 shiga Amurka

SERAP ta rubuta wa Trump wasikar neman ya haramta wa gwamnoni 7 shiga Amurka

Wata kungiya mai rajin kare hakkin jama'a (SERAP) ta rubuta wata budaddiya wasika zuwa ga shugaban kasar Amurka, Donal Trump, inda ta nemi ya yi amfani da wata dokar kasar Amurka domin haramta wa wasu gwamnoni da manyan ma'aikatan gwamnatin Najeriya shiga kasar Amurka na wucin gadi.

SERAP ta bukaci Trump ya umarci jakadan kasar Amurka a Najeriya ya isar da sakon haramtawa gwamononin shiga kasar Amurka saboda suna amfani da damar da ke hannunsu wajen cin zarafin 'yan jarida da kafafen yada labarai da ke fallasa cin hancin da ake zarginsu da hannunsu a ciki.

A cikin wasikar da SERAP ta wallafa a ranar 30 ga watan Oktoba, kungiyar ta ce siyasa ta dogara ne da bayyana wa jama'a bayanai a kan al'amuran gwamnati tare da bayyana cewa alhakin 'yan jarida ne da kafafen yada labarai su bayyana wa jama'a abinda yake faruwa domin tabbatar da samun shugabanci nagari.

SERAP ta kara da cewa yana daga cikin bangaren walwalar jama'a a sanar da su yadda ake gudanar harkokin gwamnati, saboda gwamnati ta jama'a ce ba shugabanni kadai ba.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Lawan ya bawa Atiku da Buhari shawara

"Mu na da rahotanni a kan kai wa 'yan jarida da kafafen yada labarai hari a wasu jihohin Najeriya, saboda kawai suna bayyana zargin da ake yi wa shugabanni da hannu a cin hanci. Jihohin sune kamar haka: Kuro Riba, Abia, Ebonyi, Kano, Jigawa, Bauchi, da Kaduna," a cewar wasikar SERAP mai dauke da sa hannun mataimakin darekan kungiyar, Kolawole Oluwadare.

Gwamnonin jihohin da kungiyar ta ambata sune; Farfesa Ben Ayade (Kuros Riba), Okezie Ikpeazu (Abiya), Dave Umahi (Ebonyi).

Ragowar sune; Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Kano), Mohammed Badaru Abubakar (Jigawa), Bala Mohammed (Bauchi), da Nasir El-Rufa'i (Kano).

SERAP ta ce tana fatan Trump zai amsa bukatarsu na haramtawa gwamnonin shiga kasar Amurka domin ya zama darasi ga masi muzgunawa 'yan jarida da kuma yunkurin hana a bayyana wa jama'a al'amuran gwamnatinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel