Wannan abin kunya da yawa yake: Bidiyon wata mata ta hada kai da 'ya'yanta sun yiwa ubansu dukan tsiya saboda ya cinye musu abinci a gida

Wannan abin kunya da yawa yake: Bidiyon wata mata ta hada kai da 'ya'yanta sun yiwa ubansu dukan tsiya saboda ya cinye musu abinci a gida

- An hasko wata mata da ta hada kai da 'ya'yanta suka yiwa mahaifinsu dukan kawo wuka

- An nuno matar dai suna rigima da mijin nata saboda zargin da take yi masa na cinye musu abinci wanda ta dafa da kudinta

- Wannan rikici na su dai sai da ya fito da su har bakin titi, inda a karshe mutanen unguwar suka shiga tsakaninsu suka raba rigimar

An wallafa wani bidiyo da aka nuno wata mata tana dambe da mijinta bayan ta zarge shi da cinye musu abincin da ta girka da kudin ta.

Suna cikin wannan rikici sai ga 'ya'yansu suma sun shigo rigimar inda suka yiwa uban taron dangi a yayin da shi kuma yake kokarin dukanta da itace, wannan rikici da suka fara ya sanya sun fito har bakin titi, inda mutane unguwar suka taru a kansu suna kallon ikon Allah.ka

Sai dai karshen rikicin ya zo bayan wasu daga cikin makwabtansu sun shiga tsakani sun raba rigimar.

KU KARANTA: Wa'iyazubillahi An gano bidiyon wani mutumi yana zina da bishiyar ayaba

An bayyana cewa wannan rikici dai ya faru ne a Nekede cikin jihar Imo dake yankin kudu maso kudancin Najeriya.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya faru a kasa domin samun karin bayani dangane da wannan rikici:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel