Hukuncin Kotun koli: Lawan ya shawarci Atiku da PDP

Hukuncin Kotun koli: Lawan ya shawarci Atiku da PDP

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya yi kira ga jam'iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, da su karbi hukuncin da kotun koli ta yanke a kan karar da suka daukaka.

"Ya kamata masu kara su karbi hukuncin da kotun koli ta yanke, su kuma wadanda suka samu nasara kamata ya yi su nuna dattako ta hanyar cigaba da tafiya tare da 'yan hamayya a matsayin abokai na siyasa da za a taru gaba daya a gina kasa tare," a cewar Lawan.

Shugaban majalisar dattijan ya ce hukuncin da kotun kolin ta yanke ya cire duk wani shakku da wani ko wasu ke da shi dangane da sahihancin zaben shugaban kasa da aka gudanar a 2019.

"Tun da yanzu duk wata maganar shari'a ta kare, kamata ya yi mu hada kai wajen bawa shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, goyon baya a kokarin da yake yi na gina kasar da dukkan mu zamu kasance masu alfahari da ita," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Yadda dangina suka kai ni haramtacciyar cibiyar horo daga zuwa ganin gida daga Turai - Dakta Hassan Yusuf

Lawan ya bawa shugaba Buhari da gwamnatinsa shawarar su cigaba da mayar da hankali wajen ganin sun sauke nauyin da ke wuyansu na inganta rayuwar 'yan Najeriya da dora kasa a kan tafarkin cigaba.

Ya ce majalisa ta 9 zata cigaba da samar da dokoki masu ma'ana domin inganta alakar da ke tsakanin hukumomin gwamnati da kuma tabbatar da samun hadin kai, kwanciyar hankali da cigaban Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel