Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

A yau Laraba ne 30 ga watan Oktoban 2019 kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasar ta na zaben Fabrairun 2019, Atiku Abubakar suka shigar da kara na kallubalantar nasarar Shugaba Muhammadu Buhari. A kan hakan ne wani mai tantance labarai a shafukan intanet Sunday Oguntola ya yi sharhi kan lamarin kamar yadda The Nation ta wallafa.

Abin kamar kiftawar ido. Kotun koli a ranar Laraba ta yi watsi da daukaka karar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar suka yi. Karar na kalubalantar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Babu tantama, kungiyar alkalai 7 da suka saurari shari'ar a yau sun bayyana cewa, babu amfanin daukaka karar.

Abin ya faru a lokacin da bai kai sa'a daya ba inda alkalan suka kori karar yare da bayyana cewa zasu sanar da dalilin yin hakan a ranar da zasu sanar ba da dadewa ba.

Hukuncin ya datse duk wani fadan shari'a da ke tsakanin Atiku da shugaban kasa Buhari. Amma kuma akwai sauran hanyoyin da Atiku zai iya bi don cika burinsa na zama shugaban kasa. Wadanne hanyoyi ne?

DUBA WANNAN: Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Zai fara shirin takara a zaben 2023? Amma kuma, a lokacin shekarunsa zasu kai 76. Anya ba zai yi wa Najeriya tsufa ba?

Idan Atiku ya yanke shawarar takara a 2023, ya ya zai yi da yankunan kasar nan? Akwai yuwuwar arewa zata cigaba da mulki bayan tayi shekaru 8 a jere tana mulkar kasar nan? Me zai faru da burikan 'yan kudancin kasar nan na karbar mulki a 2023?

Shin tsohon mataimakin shugaban kasar zai yi kwarjini ko a PDP din a shekarar 2023? Akwai gwamnoni da yawa a PDP da ke rainon burinsu na zama shuwagabannin kasa ko mataimaka. Za su duba girma da arzikin Atiku don sadaukar da burikansu?

Ko kuma Atiku zai bar PDP ya kafa jam'iyyarsa mai karfi da za ta sa ya cika burinsa? Idan yayi hakan kuwa, anya ba za a ce ya cika tsalle-tsalle ba? Ganin ya bar jam'iyyar ACN a 2007, 2011 ya koma PDP, 2014 ya koma APC, 2018 ya koma PDP inda ya amshe tikitin takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar.

Wanne kallo masu saka kuri'a za su yiwa Atiku idan ya kara tsayawa takarar?

Babu shakka Atiku na da tunane-tunane masu tarin yawa da yakamata ya yi a kan abinda ya dace ya yi sakamakon nakasar da ya samu a bangaren siyasarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel