Ku bayyana dalilan ku a kan hukuncin da kuka zartar - PDP ta kalubalanci kotun koli

Ku bayyana dalilan ku a kan hukuncin da kuka zartar - PDP ta kalubalanci kotun koli

- Jam'iyyar PDP ta bukaci alkalan kotun koli su sanar da 'yan Najeriya dalilan da yasa su kayi fatali da karar da Atiku Abubakar da jam'iyyar ta shigar ba kallubalantar nasar Shugaba Muhammadu Buhari

- Jam'iyyar ta PDP ta ce hukuncin da kotun kolin ta yanke ya saba da abinda mafi yawancin 'yan Najeriya da su kayi zabe suke tsammani

- Jam'iyyar ta ce tunda babu wata kotun da ta ke gaba da kotun kolin za ta hakura kuma tana fatan 'yan Najeriya da jikokin mu da za a haifa a gaba za su yabawa kokarin da ta yi

Jam'iyyar Democratic Party (PDP) ta bukaci kotun koli ta bayyana dalilan da suka saka ta yi watsi da karar da jam'iyyar da dan takarar ta na shugaban kasa a ranar 23 zaben watan Fabrairun 2019, Atiku Abubakar ya shigar na kallubalantar nasarar Shugaba Muhammadu Buhari.

DUBA WANNAN: Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar, Kola Ologbondiyan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya ce jam'iyyar ta kadu game da hukuncin da kotun ta zartar amma ta yabawa 'yan Najeriya kan goyon baya da suke bawa jam'iyyar.

Ya ce, "Tabbas, abinda muka gani yau ba shine abinda mafi yawan 'yan Najeriya da suka yi zabe kuma saka sanya ido kan yadda zaben shugaban kasa ya gudana ke tsammani ba har ma da wasu 'yan jam'iyyar ta APC.

"Jam'iyyar ta PDP ta gabatar da hujojji kwararra masu da ke nuna cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben shugaban kasa hakan yasa ta yi mamakin ganin alkalan kotu koli ba su tabbatar da hakan ba; sai dai babu wata kotu da ta 'dara wannan a kasar."

Jam'iyyar ta kara da cewa, "Duk da hakan, muna fata 'yan Najeriya da jikokin mu da za a haifa a nan gaba za su yabawa kokarin da mu kayi."

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel