Ya kamata Atiku da PDP su rungumi kaddara - Sanata Ahmad Lawan

Ya kamata Atiku da PDP su rungumi kaddara - Sanata Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya yi kira ga jam’iyyar PDP, da dan takararta a zaben shugaban kasa na 2019, Alhaji Atiku Abubakar da su rungumi kaddara su dangame da hukuncin kotun koli.

A ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba ne kotun koli ta yi watsi da karar da Atiku ya shigar gabanta inda yake kalubalantar nasarar da Buhari ya samu a zaben shugaban kasa, tare da kalubalantar hukuncin kotun sauraron koken zaben shugaban kasa da ta tabbatar da nasarar Buhari.

KU KARANTA: An gano wasu yara Musulmai 2 da aka sace daga Gombe aka sayar dasu a jahar Anambra

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito Ahmad Lawan, ta bakin kaakakinsa, Ola Awoniyi ya bayyana cewa tunda dai a yanzu shari’a ta kare, kamata ya yi a dawo a mara ma shugaban kasa Buhari baya domin ya ciyar da kasar nan gaba.

“Masu kara su rungumi kaddara, sa’annan su kuma wanda suka yi nasara su kusanci masu kara domin a zauna lafiya, a yi aiki tare wajen muhimmin aikin gina kasa.” Inji shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Daga nan Sanatan ya yi kira ga shugaba Buhari da gwamnatinsa dasu mayar da hankalinsu wajen gudanar da sahihin mulki domin tabbatar da an cimma manufofin shugaban kasa na inganta rayuwar dan Najeriya da daura kasar nan a kan turbar cigaba mai daurewa.

Daga karshe Sanatan ya bada tabbacin majalisar ta 9 a karkashin jagorancinsa za ta cigaba da samar da dokoki masu kyau tare da kokarin kulla kyakkyawar alaka tsakaninta da sauran bangarorin gwamnati don samar da zaman lafiya, hadin kai da cigaba a tsakanin yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel