An gano wasu yara Musulmai 2 da aka sace daga Gombe aka sayar dasu a jahar Anambra

An gano wasu yara Musulmai 2 da aka sace daga Gombe aka sayar dasu a jahar Anambra

Rundunar Yansandan jahar Anambra ta ceto wasu kananan yara guda biyu da wasu miyagun gungun mutane 3 suka sace su daga jahar Gombe, suka yi awon gaba dasu zuwa jahar Anambra.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Yansanda sun bayyana sunayen miyagun barayin mutanen kamar haka; Patience Opia yar asalin jahar Cross Rivers, Ejece Obi daga jahar Anambra sai kuma Blessing John daga jahar Bauchi.

KU KARANTA: El-Rufai ya bayyana hanyar da ya bi don samun bashin $350m daga bankin duniya

Da yake zantawa da manema labaru yayin da yake bayyana yaran da aka ceto, kwamishinan Yansandan jahar Anambra, John Abang ya bayyana cewa sun samu nasarar ceto yaran ne ta hanyar samu tare da tattara bayanan sirri.

A jawabinsa, Abang yace shugabar barayin mai suna Blessing John, tana ikirarin cewa it ace mahafiyar guda daga cikin yaran, yayin da tace shi kuma dayan yaron, yaran kanwarta ce wanda ta rasu.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, Haruna Mohammed ya bayyana cewa ba zasu saki yaran ga kowa ba har sai sun gudanar da cikakken bincike sun tabbatar da gaskiyar cewa iyayensu ne na hakika kafin su mikasu.

Kaakakin ya cigaba da cewa Blessing da abokan tafka ta’asanta sun kammala shirin sayar da kowanne yaro daya a kan kudi N750,000 kafin Yansanda su tarwatsa shirinsu.

A wani labarin kuma, a kokarin shirya taron bikin ranar kauyawa, tafasashshen fate ya kwaranye a kan wasu kananan yara guda biyar, inda ya kashe yara uku, sa’annan ya jikkata sauran yara guda 2 a jahar Bauchi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel