Kuma dai, an sake garkuwa da wani babban Alkalin kotun afil, an kashe dogarinta

Kuma dai, an sake garkuwa da wani babban Alkalin kotun afil, an kashe dogarinta

An sake garkuwa da wata Alkalin kotun Najeriya, shiyar Benin, Chioma Nwosu, da safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2019 a hanayar Benin-Agbor, jihar Edo.

An kashe dan sanda dogarinta a wajen.

Kwamishanan yan sandan jihar Edo, Mohammed DanMallam ya bayyanawa manema labarai cewa na kaddamar da kokarin cetosa da damke yan barandan.

Shugaban yan sandan ya ce masu garkuwa da mutanen sun kaiwa Alkalin hari ne a kan titi ta hanyar bude musu wuta. Dan sandan ya mutu a take kuma an yi anyi yunkurin tuntubar iyalinsa.

Wannan garkuwa da Alkalin ya biyo bayan satar Alkalin babban kotun tarayya dake Akure, Abdul, yayinda yake komawa daga Abuja.

SHIN KA SAN Alkalan Najeriya da INEC na da rauni - Atiku ya yi tsokaci kan faduwarsa

A ranar 25 ga Oktoba, masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Alkalin babban kotun tarayya dake Akure, birnin jihar Ondo, Justice Abdul Dogo.

An sace Alkali Abdul Dogo a ranar Talata yayinda yake hanyar komawa garin Akure daga birnin tarayya Abuja.

An samu rahoton cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Alkalin kuma sun bukaci N50 million kudin fansa.

Amma bayan kwana daya, sun sako shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel