Yadda dangina suka kai ni haramtacciyar cibiyar horo - Dakta Hassan Yusuf

Yadda dangina suka kai ni haramtacciyar cibiyar horo - Dakta Hassan Yusuf

Wani mutum mai digiri uku (PhD) da aka kubutar tare da sauran jama'a a wata cibiyar addini ta horon kangararru a Kaduna ya bayyana yadda danginsa suka kai shi cibiyar.

Mutumin, Dakta Hassan Yusuf, mai digiri na uku a bangaren ilimin tattalin arziki, ya ce danginsa sun kai shi cibiyar ne bisa zargin cewa ya zama Kirista.

Dakta Yusuf ya ce danginsa sun kai shi cibiyar a Kaduna sun jibge shi a lokacin da ziyarce su bayan ya dawo Najeriya.

"Sun ce na zama Kirista saboda na shafe shekaru 16 a Ingila, na yi aure a can. Na zo Najeriya domin fara gina muhallin da zan zauna tare da iyalina idan na dawo Najeriya. Amma sai dangina suka je suka sanar da masu cibiyar cewa na koma Kirista kuma zan bar 'ya'yana su zama Kiristoci.

DUBA WANNAN: Ta leko ta koma: Kotun daukaka kara ta kwace kujerar Tambuwal

"Kawai na tsinci kai na a cibiyar wata rana da daddare, kimanin shekaru biyu da suka wuce," a cewarsa.

Dakta Yusuf ya ce a daure suke a cibiyar kuma ana barinsu da yunwa. Ya kara da cewa yana da ciwon sukari, amma bai kara shan magungunansa ba tunda aka kai shi.

Kazalika, wani mutum mai digiri biyu da aka samu a gidan horon ya ce bai san dalilin da yasa iyayensa suka kai shi cibiyar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel