An saki sufeton dan sanda da wasu mutum 2 da aka sace bayan an biya N2m

An saki sufeton dan sanda da wasu mutum 2 da aka sace bayan an biya N2m

Yan bindiga sun saki sufeton dan sanda mai suna Sylve, wani kanin tsohon Shugaban karamar hukumar Kuje, Alhaji Mohammed A. Galadima da Nnengbe Mundi, bayan an biya naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an sace mutanen su uku daga garin Rubochi s tsakanin ranakun Juma’a da Asabar na makon da ya gabata.

Wani na kusa dasu da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar das akin sufeton dan sandan da sauran mutanen biyu a hira da aka yi dashi ta wayar tarho a yau Laraba, 30 ga watan Oktoba.

Majiyar ya bayyana cewa an saki mutanen da misalin karfe 11:00 na safe bayan masu garkuwan sun karbi naia miliyan daya a matsayin kudin fansar kanin tsohon Shugaban karamar hukumar Kuje.

Majiyar ya kara da cewa masu garkuwan sun karbi N550,000 kudin fansar sufeton dan sandan da kuma N400,000 na fansar Nengba Mundi.

A cewarsa an kai kudin fansar wani jeji a kauyen Ggowodi dake karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin Katsina ta tabbatar da yar’uwar Buhari da wasu a matsayin kwamishinoni

Ya kuma bayyana cewa an siya wa masu garkuwa katin Glo na N30,000 da pakitin sigari da kuma kwalin Boska.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya, ASP Yusuf Mariam ba domin wayarta baya shiga.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel