Babbar magana: 'Yan sanda sun kama Ministan Abuja na bogi bayan ya damfari 'yan kwangila makuden kudi

Babbar magana: 'Yan sanda sun kama Ministan Abuja na bogi bayan ya damfari 'yan kwangila makuden kudi

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta birnin tarayya, ta sanar da cafke wani mutum mai shekaru 27, Mohammed Bello da ake zargi da basaja da sunan ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammad Bello.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma, ya shaidawa manema labarai a Abuja a ranar Laraba cewa wanda ake zargin ya damfari wasu mutane da sunan zai ba su kwangiloli.

Ya ce kawo yanzu wanda ake zargin da damfari mutane kudade da ya kai naira miliyan 52.

DUBA WANNAN: Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Mista Ciroma ya ce, "Wanda ake zargin ya ce ya samu wasu bayannan sirri ne don ya yi aikin yi wa kasa hidima a hukumar Federal Capital Territory Administration, FCTA.

"An kwato wasu abubuwa daga hannunsa da suka hada da Peugeot mai lamba ABJ 856 SU, a dai-daita sahu guda daya mai lamba KEF 807 WT da tv kirar Samsung mai fadin inchi 46 da kwanuka daga wurin Bello.

"Sauran abubuwan da aka kwato daga hannunsa sun hada da janareta mai karfin 10,000 watts, injin wankin kaya, na'uarar kankara da ya yi ikirarin ya saya da kudaden da ya karbe hannun wadanda ya damfara."

Kwamishinan 'yan sandan ya ce jami'ansa suna nan suna bin sahun sauran wadanda ke aiki tare da shi da suka hada da wani Simon da ke basaja da sunnan Direkta a FCTA da wani Idris da ke basaja da sunan hadimin ministan.

Mista Ciroma ya kuma ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu don su zama darasi ga sauran mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel