NEC: Yemi Osinbajo ya hadu da wasu Gwamnoni a Ranar Talata

NEC: Yemi Osinbajo ya hadu da wasu Gwamnoni a Ranar Talata

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo, ya gana da sauran ‘yan majalisar sa ta NEC mai kula da tattalin arzikin Najeriya. An yi wannan zama ne a cikin fadar shugaban kasa a Abuja.

An saba yin wannan zama ne a Ranar Alhamis din karshen wata wanda a wannan karo ta fado Ranar 31 ga Wata. Sai dai an canza lokacin wannan muhimmin zama inda majalisar ta gana jiya.

Kamar yadda mu ka samu labari, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci majalisar NEC din ne a Ranar Talata. Babu wani dalili da aka bada na janye taron daga yadda aka saba a Ranar Alhamis.

A tsarin mulkin Najeriya, mataimakin shugaban kasa shi ne shugaban wannan kwamiti na tattalin arziki. Duk wata kuma majalisar nan ta kan zauna da gwamnonin jihohi da na CBN.

KU KARANTA: Yadda Bankin Duniya su ka bani Dala miliyan 350 domin gyara harkar ilmi

Sauran kusoshin gwamnatin da su ke cikin wannan kwamiti sun hada da Ministar kudi da kasafi, Sakataren gwamnati, da kuma shugabannin ma’aikatun da su ka shafi harkar tattalin arziki.

Aikin wannan majalisa ta NEC shi ne lura da tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatin tarayya da kuma tabbatar da hadin-kai tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi da kananan hukumomi.

An fara taron wannan watan ne da kimanin karfe 11:00 na safe. An dauki tsawon lokaci ana tattaunawa a fadar shugaban kasar. Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya yi magana bayan zaman.

A zaman da aka yi, majalisar ta yabawa kokarin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kwamitinsa su ka yi na saukaka kasuwanci a fadin Najeriya kamar yadda alkaluma su ka nuna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel